Sabon salon ɗaukar hoton Hausawa na ta da ƙura

Al'umar Hausawa, kamar sauran mutane, suna son ƙawa da burgewa.

Suna nuna wadannan abubuwa ne ta hanyoyi daban-daban, cikin su har da irin kwalliyar da suke yi da mu'amala da mutane.

Bahaushe yana da son daukar hoto, tun daga lokacin hoton da ba shi da launi har zuwa wannan lokaci da ake yinsu kala-kala.

Wani salon hoto kuma shi ne wanda ake kira "selfie", wato "dauki-kanka" wanda yake tashe a baya bayan nan.

Sai dai babu salon hoton da ya fi jan hankalin mutane yanzu kamar wanda ake dauka hannu a dunkule kuma ana rufe fuska.

Yawanci dai ana daukar hotunan ne daga mutum daya zuwa hudu ko sama da haka.

Wannan salo na daukar hoto, wanda ake kira dab a turance, rawa ce wadda ake yi ana dunkule hannu a jefa shi baya, kamar yadda ake daukar hoton, kuma ta samo asali ne daga birnin Atlanta, na jihar Georgia da ke Amurka.

Wadanda ke daukar irin wadannan hotuna na ganin hakan tamkar wani sabon yayi ne na burge jama'a.

Sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa abincin wani, gubar wani; wasu na ganin hakan tamkar sakarci ne domin kuwa ba kasafai hotunan ke nuna fuskar mutumin da ke cikinsu ba, wanda kuma shi ne dalilin daukar akasarin hotuna.

Shin ya ya kuke ganin wannan sabon salo na daukar hoto?

Ku aiko mana da ra'ayoyinku a shafinmu na BBC Hausa Facebook