Kamfanin Microsoft ya yi nasara a kotu

Image caption Microsoft ya yi marhabin da hukuncin wanda ya ce wata babbar nasara ce na kare sirrin jama'a

Wata kotun daukaka kara a birnin New York ta zartar da hukuncin cewa gwamnatin Amurka bata da ikon tilasta wa kamfanin Microsoft bada iznin shiga rumbun adana bayanai na kamfanin da ke wasu kasashen duniya.

Ana dai kallon wannan hukunci a matsayin wani mataki na kare sirrin kamfanonin dake sarrafa na'urorin kwamfuta.

Ma'aikatan shari'a ta Amurka ta bayyana rashin jin dadin ta game da wannan hukunci.

Amurka dai na son samun damar shiga rumbun adana bayanai na kamfanin ne a kasar Ireland a wani bangare na binciken da ta ke yi kan zargin safarar kwayoyi.

Sai dai kamfanin Microsoft ya yi marhabin da hukuncin wanda ya ce wata babbar nasara ce na kare sirrin jama'a karkashin dokokin kasashen su maimakon dokoki gwamnatocin wasu kasashen waje.