Cinikin motoci ya ragu a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya, yayin da ake fama da koma bayan tattalin arziki, masu sayar da motoci musamman motoci na alfarma sun koka akan rashin ciniki a harkokin kasuwancinsu.

Wasu masu sayar da irin wadannan motoci na alfarma sun danganta rashin ciniki akan tsadar da motocin suka yi sanadiyyar tashin canjin kudaden kasashen waje da karancin kudi a hannun jama'a.

Tuni dai wasu masu saida motocin alfarma suka ce sun fara duba yiwuwar sauya sana'a.

Koda a cikin wannan makon hukumar lamuni ta duniya IMF ta ce tattalin azikin Nigeria zai ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali.