Gobara ta laƙume gidan marayu

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Gobarar ta kashe mutum takwas

A kalla mutane takwas ne suka mutu bayan da gobara ta tashi a wani gidan marayu a Afirka ta Kudu.

Gobarar wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Alhamis, a birnin Durban, ta yi sanadiyyar mutuwar yara shida da manya biyu.

Mafi karancin shekaru a cikin yaran shi ne dan shekara takwas.

Masu aikin ceto sun ce wutar ta tashi ne a bangaren yara na gidan marayun.

An shafe sa'o'i hudu kafin a kashe gobarar.

Har yanzu ana cigaba da bincike kan musabbabin abinda ya haifar da wutar.