Yadda aka kai harin Faransa

Hakkin mallakar hoto epa

Akalla mutum 84 ne aka kashe a harin da wani mutum ya kai da babbar mota a birnin Nice na Faransa - wanda shi ne mafi muni tun harin Nuwamban bara.

Kasar na cikin dokar-ta-baci tun lokacin kuma an tsaurara matakan tsaro.

Ga abinda muka sani game da yadda harin ya afku:

'Mutanen Nice sun rude'

An fara kai harin ne da misalin karfe 10.30 a gogon can wato (8.30 a gogon GMT), jim kadan bayan da dubban mutane suka kammala kallon wasan wuta a karshen bikin tunawa da ranar samun 'yan cin kai, ta Bastille Day.

An cashe a wurin inda aka yi wasannnin shawagi da jirgi.

Sai dai a daidai lokacin da mutane suka taru, sai wani mai babbar mota ya tawo a guje ya afka musu.

Daga nan ne kuma direban motar ya sake ja da baya, inda ya kara afkawa taron mutanen.

Wani dan majalisar yankin ya bayyana cewa direban ya bi takan daruruwan mutane.

Wanene direban motar?

An bayyana direban da cewa Bafaranshe ne dan asalin kasar Tunisia mai shekara 31, bayan da aka samu wasu takardun shaidu a cikin motar.

Sai dai har yanzu 'yan sanda ba su tabbatar da wannan bayanai ba.

An kuma gano bindigogi da gurneti na boge a cikin motar.

Babu tabbas ko yana aiki ne shi kadai ko kuma da tallafin wasu.

An shaida wa mutanen yankin da suka zauna a cikin gidajensu domin kaucewa yiwuwar kai wani harin.

Wannen martani shugabanni suka mayar?

Image caption Hollande ya zargi 'yan kungiyar IS

Nan take ta bayyana cewa mutane da dama sun mutu a harin.

An kwashe gawarwaki da kuma wadanda suka samu raunuka zuwa wani asibiti.

Shugaba Francois Hollande ya koma birnin Paris daga ziyarar da ya kai Avignon, inda zai hadu Firai Minista Manuel Valls domin tattaunawa kan lamarin.

Su wa ye suka kai harin?

Ba tare da bata lokaci ba Shugaba Hollande ya ce babu tantama harin na da "alaka da ta'addanci".

Masu gabatar da kara kan harkokin ta'addanci sun kaddamar da bincike kan kisan gilla a wani aikin ta'addanci da ake tunanin na hadin gwiwa ne.

A farkon makon nan ne hukumomin tsaro a kasar suka yi gargadin cewa za a iya samun karin hare-hare daga masu zazzafan kishin Islama a kasar.

Duk da cewa kungiyar IS ba ta ce ita ta kai harin ba kawo yanzu, amma ta sha kai hare-hare a Faransa tun watan Janairun 2015.