Morocco na son komawa tarayyar Africa

Image caption A shekarar 1981 Morocco ta fice daga tarayyar Africa

Jakadan kasar Morocco na musamman ya nemi shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta da ya tsoma baki wajen kokarin da Moroccon take yi na neman sake komawa mamba a tarayyar Afirka wato AU ba tare da gindaya mata wasu sharuda ba.

A shekarar 1981 ne dai Morocco ta fice daga tarayyar ta Afirka, bayan da tarayyar ta amince da cin gashin kan yankin yammacin Sahara wato Saharawi.

Shugaban na Kenyata ya ce zai yi magana da takwarorin sa kan wannan batu.

To sai dai kuma Tarayyar ta Afirka wadda take yin wani taron koli a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, ta ce za ta yi bakin kokarinta wajen ganin al'ummar yankin yammacin Sahara sun gudanar da zaben raba-gardama dangane da ficewa ko kuma ci gaba da kasancewa a Morocco.

To sai dai wasu masana kan harkokin kasashen waje kamar Malam El-Haroon Muhammad, na ganin cewa wasu kasashe ne a nahiyr ta Africa suka fara zawarcin Morokon.