"Rabin matasa a Afrika ba sa zuwa makaranta"

Hakkin mallakar hoto via afrika
Image caption Yara miliyan 99 basa samun ilimi kwata-kwata.

Hukumar raya ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ta ce akalla rabin matasa a nahiyar Afrika, wadanda shekarunsu ba su wuce goma sha biyar zuwa goma sha bakwai ba, ba sa zuwa makaranta.

UNESCO ta ce wannan adadin shi ne mafi girma a kowane yankin na duniya.

A jimlace, fiye da kananan yara miliyan casa'in da tara da suka kai shekarun shiga makarantar Firamare da sakandare ba sa samun ilimi kwata-kwata.

Hukumar ta ce akalla miliyan goma sha biyar ne daga cikin wadannan yaran kafar su ba zata taba taka cikin aji ba har tsawon rayuwar su, kuma wannan ya fi kamari ne a tsakanin yara mata fiye da maza.

Barkewar rikice-rikice da talauci da kuma kin bayar da ilimi ga mata na daga cikin dalilan da hukumar ta ce ke janyo hakan.