Afrika za ta tattauna dangantakarta da ICC

Hakkin mallakar hoto au
Image caption Cikin batutuwan da za a tattauna a taron, har da batun rashin tsaro da ya addabi kasashen Afrika

A ranar Lahadi ne shugabannin kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Afrika ke fara taro a Rwanda, kuma batun dangantakar kasashen da Kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague shi ne a kan gaba.

Shugabannin kasashen Afrika da dama sun bukaci kasashen nahiyar da su kaurace wa kotun sakamakon zargin da suke yi cewa kotun na yi wa shugabannin nahiyar bi-ta-da-kulli.

Shugabannin dai sun fi son kafa wata kotu ta musamman a nahiyar Afrika wadda za ta dinga hukunce-hukuncen da suka shafi tauye hakkin bil'adama.

Shugaban Sudan, Omar Al-Bashir, wanda ya bijire wa sammacin kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague, shi ma ya isa Kigali domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afrikan, bayan gwamnatin Rwanda ta tabbatar masa cewa ba za a kama shi ba.

Kazalika, taron na kwana biyu zai tattauna a kan rikicin Sudan Ta kudu, da kuma shirin kungiyar Tarayyar Afrika na yin fasfo na bai-daya da bai wa al'umomin 'ya'yan kungiyar damar shiga kasashen juna ba tare da takardar biza ko izini ba.