An dakile yunkurin juyin mulki a Turkiya

Mukaddashin babban hafsan sojin Turkiya ya sanar da cewa yunkurin juyin mulki a kasar bai yi nasaraba.

Janar Umit Dundar ya ce an kashe sojoji dari da hudu daga cikin wadanda suka yi yunkurin juyin mulkin.

Ya ce wasu mutanen casa'in da suka hada da 'yan sanda da fararen hula sun mutu, kuma ya bayyana su a matsayin wadanda suka yi shahada.

A daren Asabar, an yi ta harbe harben bindiga da fashewar abubuwa a biranen Ankara da Istanbul.

Jami'ai sun ce an kama sojoji fiye da dubu daya da dari biyar, kuma ana tsare da su.

Ministan Turkiya a Tarayyar Turai, Omer Celik ya ce an shawo kan kashi casa'in cikin dari na lamarin, amma har yanzu, ana ci gaba da garkuwa da wasu kwamandojin soji a kasar.