Juyin mulki: An kori alkalai 2700 a Turkiya

Image caption 'Yan kasar Turkiya

Gwamnatin Turkiya ta fara yin dirar mikiya akan kungiyoyi da dai-daikun jama'a da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin a kasar.

An kori alkalai fiye da dubu biyu da dari bakwai a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya ce alkalan suna da alaka da wani malami dake zaune a Amurka, Fethullah Gulen.

Gwamnatin ta ce wasu sojojin dake biyayya ga malamin ne suka shirya juyin mulkin da bai yi nasara ba.

An soma yunkurin juyin mulkin ne lokacin da sojojin suka fara kai hari kan wasu muhimman wurare a Istambul da Ankara da tankokin yaki da jirage masu saukar ungulu.

Sojoji kimanin dubu uku ne yanzu haka suke tsare.