Za a bullo da fasahar raba maganin AIDS

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen duniya na fafutikar ganin sun kawar da cutar

Wakilai sama da 18,000 ne suka hallara a birnin Durban na kasar Afirka ta kudu domin samar da mafita wajen yaki da cutar AIDS.

Ana sake yin taron na Majalisar Dinkin Duniya a kan cutar ta AIDS ne domin isar da wani sako da ke nuna cewa har yanzu akwai jan aiki wajen kawar da cutar.

Duk da irin ci gaban da aka samu wajen yaki da cutar a Afirka ta kudu, masu kamuwa da cutar na karuwa.

Cutar ta AIDS dai na raguwa a fadin duniya.

Za dai a kwashe kwana biyar ana wannan taro, inda likitoci da masu fafutuka da jam'an kiwon lafiya da masana kimiyya za su gabatar da makaloli da kasidu a kan irin ci gaban da aka samu a yakin da ake yi da cutar.

Babban kalubalen da masu dauke da cutar ke fama da shi shekara 16 da suka gabata shi ne karancin maganin da ke rage kaifin ta, amma a yanzu rashin kudi na daga cikin manyan matsalolin da ke kawo tsaiko a yaki da cutar.