Face Time ta taimakawa Erdogan

Shugaba Erdogan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kusan mutane 200 ne suka rasa rayukansu a juyin nulkin, ya yin da wasu kusan 1500 suka jikkata.

Wani abu da ya fito fili a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya, shi ne irin rawar da hanyoyin sadarwa na zamani suka taka a lamarin.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan dai ya yi amfani da manhajar FaceTime ta wayarsa wajen jaddada wa jama'ar kasar cewa, juyin mulkin da aka yi bai yi nasara ba, sannan ya yi kira ga jama'a su fito kan tituna domin nuna adawa da juyin mulkin.

Yayin da rahotanni ke cewa, wadanda suka shirya juyin mulkin a nasu bangaren, sun yi amfani ne da WhatsApp wajen musayar sakonni tsakanin junansu.

Jama'a kuma sun yi ta amfani da kafar bidiyo kai-tsaye na Facebook wajen nuna wa duniya abin da yake faruwa.

A ranar juma'a da ta wuce ne sojoji suka mamaye titunan yawancin biranen kasar, cikin tankokin yaki da motoci masu sulke.