Giya ta kashe leburori 17 a Indiya

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption Mutane kan sarrafa irin wannan giya ne a gida

'Yan sanda a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya sun ce wasu leburori 17 sun mutu bayan shan giya irin wacce ake sarrafawa a gida.

Mutanen sun sha barasar ne wacce aka hana shata a ranar Juma'a da daddare.

An kam wani mai sayar da barasar an kuma dakatar da jami'ai da dama.

A Indiya dai mutuwa sakamakon shan irin wannan barasa ta zama ruwan dare a kauyuka.

A watan Afrilu ma jihar Bihar ta zama ta baya-baya da ta haramta sayar da giyar.

Masu goyon bayan haramta sayar da giyar sun ce matakin na iya dakatar da shan da ake wa giyar tamkar ruwa da kuma hana faruwar rikice-rikice.

Yayin da masu adawa da matakin kuwa ke cewa hakan zai janyo a dinga shiga da barasar da ba a san ya aka yi ta ba daga wasu wurare.