Jiragen yakin Rasha sun kashe mutum 28 a Aleppo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fararen hula na cikin halin ha'ula'i a Aleppo

Kungiyar sa ido kan kare hakkin bil'adama ta Syria ta ce wasu hare-haren sama da aka kai sun yi sanadin mutuwar a kalla mutane 28 a birnin Aleppo.

Rahotanni sun ce jiragen yakin Rasha ne suka kai hare-haren da nufin samun yankunan da ke karkashin ikon 'yan tawaye a gabashin birnin.

Kamfanin dillanci labari na Faransa AFP, ya ce an yi ta jefa bama-bamai a yankuna da dama.

Cikin yankunan da bama-baman suka fada har da wani asibiti, inda marasa lafiya da ma'aikatan wajen da dama suka ji rauni.

Gwamnatin Syria ta ce 'yan tawaye sun kai hare0hare Yammacin birnin Aleppo da ke karkashin ikonta, inda mutum daya ya mutu.

Aleppo ya kasance cibiyar kasuwanci da masana'antu na Syria, amma tun shekarar 2012 ake gwabza fada a birnin.