Zawarawa da 'yan mata na son aure a Kano

Image caption Karancin kudi na cikin dalilin da ke sanyawa ake rungumar shirin na gwamnatin jihar

A Nigeria, hukumar Hizba ta jihar Kano ta ce sama da zaurawa da 'yan mata fiye da dubu goma ne suka yi rajista domin su amfana daga tsarin nan na auren Zaurawa da 'yan mata, wanda gwamnatin jihar ke shiryawa.

Masu shirya auren sun ce matakin na taimakawa wajen rage adadin zaurawa da 'yan mata da ke neman mazan aure.

Sai dai wannan na faruwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke kukan karancin kudin shiga.

Yawancin matan da suka yi rijistar sun shaida wa BBC cewa matsin rayuwa da rashin abin da za su tare a gidan miji -- kamar gado da katifa -- su ne suka sanya su shiga wannan tsari domin su samu tallafi.

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ke aurar da zawarawa da 'yan mata ba a jihar, kuma masu kudi da 'yan kasuwa na kawo ta su gudummawar.