Mene ne burinku a rayuwa?

Image caption Ko wanne dan adam yana da buri, sai dai na wani ya bambanta da wani

Ko wanne dan adam yana da buri a rayuwarsa, kuma Hausawa na cewa buri ba ya karewa sai ranar da rai ya yi halinsa.

Wasu burinsu su zama shahararrun Malamai ko fitattun masu kudi, ko shahararrun 'yan kwalo, ko minista, ko shugaban kasa, ko gwamna, ko sanata, ko fitaccen dan fim.

Wasu nasu burin ma bai kai wadancan ba, ba zai wuce son ganin sun yi aure ba, wasu kuwa samun haihuwa ne burinsu, wasu so suke su je yawon shakatawa wasu kasashen, wasu burinsu su kammala karatu.

Akwai masu burin zama likita, ko injiniya, ko matukin jirgin sama, ko samun aiki da dai sauransu.

Yayin da mutane da dama ke da burikan da suka shafi duniya, ba za a rasa wadanda nasu burin ya ta'allaka ne da samun lahira ba kawai.

A kan haka ne sashen Hausa na BBC ya kaddamar da wani sabon shiri wanda zai baku damar turo mana da hoton bidiyo kan irin burin da kuke da shi a rayuwarku.

Muna bukatar ku aiko mana da hotunan biyonku wanda bai wuce tsawon minti guda ba, dauke da burin naku.

Za mu wallafa bidiyon da suka yi kyau a shafinmu na BBChausa.com

Idan ba za ka iya daukar bidiyo ba, nadi muryarka sai ka turo mana tare da hotonka.

Za ku iya turo mana bidiyo ko muryar da kuka nada ta lambarmu ta WhatsApp 08092950707.

Ko wanne dan adam yana da buri a rayuwa, kuma Hausawa na cewa buri ba ya karewa sai ranar da rai ya yi halinsa.

BBC Hausa
Getty

Wannan shiri zai ba ku damar sanin cewa lallai burin mutane ya bambanta kamar yadda suka bambanta a siffa.

Kuma ta haka ne za ku gane cewa idan kai burinka babba ne, to wasu nasu burin bai taka kara ya karya ba.

Ku kasance tare da BBC Hausa a kowanne lokaci.