An fara taron Republican da hayaniya

Mista Trump
Image caption Kawuna sun fara daukar dumi a daidai lokacin da ake gab da yin babban zabe a Amurka.

An bude babban taron jam'iyyar Republican cike da hayaniya, kuma bikin bude taron ya kai kololuwarsa ne lokacin da dantakarar shugaban kasar jam'iyyar, wato Donald Trump ya bayyana.

Bisa al'ada dai dantakara ba ya zuwa wajen taron sai bayan an kammala matakan tabbatar masa da takarar tasa, amma Donald Trump sai ya yi kasadar zuwa wajen domin ya gabatar da Iyalinsa, Melania.

Ta shaida wa taron cewa Mijinta gwarzo ne da ba zai kunyata Amurkawa ba.

Sai dai tun ba a je koina ba bikin ya samu cikas, hayaniya ta kaure, sakamakon boren da wasu wakilai suka yi, wadanda aka hana musu damar yin korafinsu na adawa da tsayar da Mr Trump a matsayin dantakarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican, inda suka yi ta masa eho da gwalo.

Daya daga cikin wakilan da ke halartar taron mai suna Melanie Sturm ta ce abin da Donald Trump ya shuka ne yake girba