UNICEF: Dubban yara a Borno na fama da yunwa

Kananan yara a sansanin 'yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto msf
Image caption UNICEF ta gargadi cewa yaran ka iya mutuwa idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

Wani sabon rahoto da Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna cewa kusan yara dubu dari biyu da hamsin da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Borno da ke arewacin Najeriya ke fama da rashin abinci mai gina jiki.

UNICEF ta yi gargadin cewa dubbai a ciki za su mutu matukar ba a dauki matakan gaggawa ba dan ceto rayuwarsu.

Wuraren da UNICEF ta kai ziyara, da kuma a baya mayakan Boko Haram ke iko da su ta samu mutanen da ke zaune a wurin na rayuwa babu ruwan sha da abinciki da cikakkiyar tsafta.

A watan da ya gabata an gabatar da rahoton 'yan gudun hijira na cikin mawuyacin hali na rashin abinci, inda wasu suka rasa rayukansu saboda tsananin yunwa.

Rahoton ya kara da cewa ya yin da sojojin Najeriya ke kara dannawa kauyukan da 'yan Boko Haram suka mamaye, tare da fatattakarsu ake kuma samun damar kai agaji yankunan matsalar rashin abinci mai gina jiki ga mutanen da ke wadannan yankuna na kara fitowa fili.

UNICEF ta ce cikin yara 2440 da ke fama da rashin abinci maigina jiki a jihar Borno, daya cikin biyar ka iya mutuwa idan har ba a yi gaggawar taimaka musu ba.

Jami'in UNICEF mai kula da shiyyar yammaci da tsakiyar Afurka Manuel Fontaine yace wasu yaran 134 ka iya mutuwa a kowacce rana saboda cututtuka masu nasaba da abinci mara gina jiki, ya yi kira ga dukkan kasashe, da kungiyoyin bada agaji da su shigo cikin lamarin dan ceto rayuwar yaran da kuma kare sauran yara daga fadawa hadarin da su ke ciki.

Mista Fontaine ya kara da cewa a kauyukan da suka ziyarta a jihar Borno, ya ga kauyukan da 'yan Boko Haram suka daidaita amma duk da haka mutane na zaune a cikin su a mawuyacin hali, dubban yara kanana sun yi zuru-zuru saboda rashin abinci cikin tsananin bukatar taimako.

A karshe rahoton yace har yanzu akwai mutane miliyan biyu da har yanzu UNICEF ta gagara isa inda suke, wanda hakan ke nuna ta yiwu matsalar da kananan yaran ke ciki ta karu idan aka isa inda suke.

Shekaru bakwai da mayakan Boko Haram suka yi su na cin karen su abbu babbaka a arewa maso gabashin Najeriya da makasashe Makofta, ya hallaka sama da mutane 20,000 ya yin da fiye da miliyan biyu suka rasa muhallansu.