'Yar Nigeria ta lashe gasar Komla Dumor

Didi Akinyelure
Image caption Akinyelure ta kware wurin bayar da labaran kasuwanci

Wata 'yar jaridar Najeriya ta lashe gasar Komla Dumor wacce gidan talabijin na BBC World News ya sanya kan 'yan jaridar da suka fi iya bayar da labarin da ya shafi Afirka.

Didi Akinyelure, 'yar jarida ce da ke gabatar da labaran kasuwanci ta gidan talabijin na CNBC, wanda ke watsa labarai a dukkan sassan nahiyar Afirka.

A watan Satumba ne za ta soma aiki da BBC a hedikwatarmu da ke London na tsawon wata uku.

An kaddamar da gasar ne domin nuna girmamawa ga Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye da rahotanni na tashar BBC mai watsa labarai ga sassan duniya, wanda kwatsam ya mutu a shekarar 2014, yana da shekara 41 a duniya.

Ms Akinyelure ta ce tana matukar kaunar yadda Mr Dumor yake gabatar da shirye-shirye.

Image caption Komla Dumor ya rasu ne kwatsam a shekarar 2014

Ta kara da cewa Mr Dumor "yana bayar da labarai kan Afirka cike da karsashi da rashin nuna bambanci, lamarin da kan sa mutane shauki."

Daya daga cikin alkalan da suka zabi Ms Akinyelure, Josephine Hazeley, ta ce Ms Akinyelure ta yi fice wajen bayar da labaran kasuwanci, "wadanda shi ma Komla ya yi matukar kwarewa wajen bayar da su".

Ms Akinyelure ce ta biyu da ta lashe gasar, inda wata 'yar jaridar Uganda Nancy Kacungira ta lashe a karon farko.