An kashe sojojin Faransa a Libya

Image caption Ana zargin wata kungiyar 'yan bindiga ne suka harbo jirgi mai saukar ungulun

Ma'aikatar tsaro ta Faransa ta ce sojojinta uku sun mutu a Libya, bayan da aka harbo jirgi mai saukar ungulun da suke ciki.

Wata gajeriyar sanarwa daga ma'aikatar ta fitar ta ce sojojin sun mutu ne a lokacin da suke tsaka da bautawa kasa.

Da safiyar ranar Laraba ne, mai magana da aywun ma'akatar tsaron Faransan, Stephane Le Foll , a karon farko ya tabbatar da cewa dakarun kasar na musamman suna Libya.

A ranar Talata ne kamfanin dillancin labarai na AP, ya ambato jam'ian Libya na cewa wasu 'ya bindiga sun harbo jirgin mai saukar ungulu na Faransa.

Harin ya faru ne a ranar Lahadi kusa da birnin Benghazi, kuma babu wanda ya tsira.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce sojojin "na gudanar da wani muhimmin aikin leken asiri ne" lokacin da aka kaimu harin.

Kawo yanzu babu wata kungiyata da ta dauki alhakin harbo jirgin, amma akwai masu tayar da kayar baya da dama a Gabashin kasar ta Libya.