Nuhu Ribadu zai koma APC

Image caption 'Yan siyasar Najeriya sun yi kaurin suna wajen sauya sheka

Tsohon dan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar ACN, Malam Nuhu Ribadu, na shirin komawa jam'iyyar APC, mai mulkin kasar.

Malam Nuhu, wanda ke daya daga cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar ta APC, ya fice daga cikinta ne gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2015, inda ya koma jam'iyyar PDP, mai mulki a wancan lokacin.

Tsohon shugaban hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annatin ya tsaya takarar gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar ta PDP, kodayake ya sha kaye a hannun Jibril Bindawo, gwamnan jihar na yanzu.

Wata majiya da ke kusa da Malam Nuhu Ribadu ta shaida wa BBC cewa tsohon shugaban na EFCC zai sake karbar katin shiga jam'iyyar APC a karshen makon da muke ciki.

Muhimman bayanai kan Ribadu

2003

Shugaban hukumar EFCC

2011

Takarar shugaban kasa a ACN

  • 2013 Da shi aka kafa APC

  • 2014 Ya sauya sheka zuwa PDP

  • 2016 Ya koma APC

Getty

'Yan siyasar Najeriya dai sun yi fice wajen sauya sheka da zarar sun ga ba za su cimma burinsu ba a inda suke.

Kawo yanzu babu tabbas kan dalilan da suka sa Ribadu komawa jam'iyyar ta APC, wacce ya fice daga cikinta ba zato ba tsammani.