Trump ne dan takarar Republican

Donald Trump
Image caption Yanzu kuma sai jiran babban zabe da ke tafe.

An tabbatar da Donald Trump na jam'iyyar Republican a matsayin dantakarar shugaban Amurka a zabe mai zuwa.

Ya yi nasarar ne a babban taron jam'iyyar da aka yi a birnin Ohio, bayan samun isassun kuri'un da aka kada na jiha-jiha a zaben fidda gwani.

A gobe Alhamis ne ake saran zai gabatar da jawabin godiya ga wakilan jam'iyyarsu da suka zabe shi.

A yanzu kallo ya koma sama, kawuna za su kara daukar zafi a daidai lokacin da babban zaben kasar ke tafe, da ake kokawar karbar iko tsakanin Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrats da Donald Trump na jam'iyyar Republican, zaben da aka dade ana jira saboda 'yan takarar da ke fafatawa fitattun mutane a Amurka.

Kuma tuni abokan arziki suke ta tururuwar yiwa mista Trump din murna ta shafukan sada zumunta da muhawara, dan mista Trump Donald Junior shi ne ya fara wallafa kalaman fatan alkhairi ga mahaifinsa jim kadan bayan sanar da nasarar da ya samu.