Gwamnatin Turkiya ta kafa dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto bbc

Shugaban Turkiya Racep Tayyip Erdogan ya kafa dokar ta-baci ta tsawon wata uku, sakamakon yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a makon jiya.

Shugaba Racep ya ce matakin zai bai wa hukumomi damar daukar mataki nan take a kan mutanen da ke da hannu a lamarin.

A wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin bayan ya yi wata ganawa da sojoji masu basu shawara, shugaban ya yi alkawarin magance matsalar da dimokradiyya ke fuskanta, sannan a lokaci guda kuma, ya ce zai kare muhimman 'yancin da Turkawa ke da su.

Dokar ta-bacin za ta bai wa shugaban kasa damar yin gaban kan sa ba tare da ya tuntubi majalisa ba, sannan zai iya takaitawa ko ma share duk wasu hakkoki da ake da su.

Za kuma a iya amfani da dokar wajen ci gaba da tsare mutane sama da dubu goma da aka kama tun bayan yunkurin juyin mulkin.

Bayan ayyana dokar Mt. Erdogan ya ce ko kadan ba ta ci karo da dimokradiyya ba, da dokokin kasar, da kuma hakkin jama'a.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin dai gwmnatin ta Turkiya ta dauki matakan ba sani ba sabo kan sama da mutane dubu hamsin, inda aka kama wasu, wasu kuma aka kore su daga aiki, aka dakatar da su, yayin da kuma aka rufe makarantu sama da dari shida.