An kama 'yan majalisar dokokin Zamfara

Hakkin mallakar hoto google

Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce gwamnan jihar Abdul Aziz Yari ya san an kama kakakin majalisar dokoki da wasu shugabannin majalisar.

Sai dai wasu jaridun kasar sun ambato gwamnan yana musanta hannu a kama 'yan majalisar.

Daya daga cikin 'yan majalisar Mansur Ahmad Musa Bungudu ya shaida wa BBC cewa gwamnan ya san hukumar tsaro ta farin-kaya, DSS ta kama wasu 'yan majalisar ne saboda yana tsoron kada a tsige shi sakamakon rabin aikin da yake yi.

A cewarsa, Gwamna Yari, ya daina zama a jihar domin yi wa talakawa aiki, yana mai cewa ya cika yawon tsiya.

Dan majalisar ya kara da cewa wasu takwarorinsa sun tsere daga jihar domin gudun kada gwamnan ya sa a kama su.

A wata ganawa da manema labarai da wasu 'yan majalisar suka yi a Kaduna, sun nuna rashin jin dadin dangane da yadda gwamnan ke gudanar da al'amurra a jihar, musamman rashin biyan albashin ma'aikata, da rashin bin dokokin tafiyar da gwamnati.

Mansur Ahmad Musa Bungudu ya musanta zargin cewa suna kai ruwa rana da gwamnatin jihar ne domin biyan bukatun kansu kawai.