BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 14:50 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Sanin Ya Kamata
 
Dan gwagwarmaya

Lalle a koyaushe a BBC mu yi kokarin ganin ba mu saba ma wani ko wasu ba wajen kiransu da sunaye ko lakubban da ba za su yi marhabin da su ba.

Jin wasu mutane suna amfani da wasu kalaman muzantawa, wulakanci ko ba’a ba hujja ba ne a gare mu mu ma yi haka.

Ko da an sàba da sunan, shi kuma wanda ake kira ya daina fada a kan haka don babu yadda za ya yi, lalle mu mu yi kokarin kaucewa, mu kira shi abin da ya fi so.

Kada kuma mu yi ma wata al’umma kudin goro wajen kakaba mata laifin da wani ko wasu daga cikin ta suka aikata.

Haka kuma kiran wani da sunan wata nakasar da yake da ita don ba’a ko muzanatawa maimakon sunansa na ainihi, ba abin amincewa ba ne.

Amma kuma mu yi hattara kada wajen neman kiba ka samo rama.

Idan mutum ya kira kansa da wani mugun suna kamar na zàgi alal misali, wanda bai kamata mu ma maimata ba.

Lalle mu kauce ma duk wani abu da ya saba ma da’a ko natsuwar jama’a, irin su ashariya da batsa.

A abin da ya shafi mutuwa kuma, mu kauce ma kalmomin da suka yi kama da nuna rashin damuwa.

Kada mu ce, “an yi masa yankan rago” bayan kuma “an yanka shi” ya isa, ba tare da mun hada rasuwarsa da ta dabba ba.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri