BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 14:59 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Nahawu
 
Nahawu

Sanin nahawun harshen da kake magana da shi babban jagora ne wajen isar da sakon da kake son isarwa.

Idan ya kasance ba daidai ba sakon sai ya je ba daidai ba. Watakila ma a kasa fahimtarsa baki daya.

Yi amfani da Hausar da galibin masu sauraronka za su fahimta.

Hakan yana nufin wani lokacin sai ka yi hakuri da Hausar garinku idan galibin masu saurare ba za su fahimci abin da kake nufi ba, ka kuma rungumi wadda galibin jama’a za su fi fahimta.

Kwarya kuma ta bi kwarya, idan abu mufuradi ne kamata ya yi abin da zai siffanta shi ko bayyana aiki game da shi ya kasance mufuradi. Jam’i kuma ya bi jam’i.

Misali, “jirgi ya...”, “jirage sun...”, “giwa ta sha..”, “giwaye sun sha..”.

Haka kuma a siffantawa, “kyakkyawan mutum” amma ba “kyakyyawan mace” ba. Sai dai a ce “kyakkyar mace”, siffar macen ta kare da “r” ta namiji kuma ta kare da “n”.

A jinsi na abubuwa masu rai babu wahalar bambancewa tsakanin wanda za ka baiwa lamirin mace ko namiji wajen nuna dangantaka.

Za a yi amfani da “na” ga namiji, “ta” kuma ga mace. Misali, “zakarana”, amma “kazata”.

Su kuma ababen da ba halittu masu rai ba, wani abin da zai taimaka wajen gane ko jinsin mace ne ko na namiji, shi ne cewa galibin jinsin mace yana karewa da harafin “a”.

Misali, gargajiya, tunya, shawara, fassara, kwarya, garka, garkuwa, duka lamirin mace suke da shi.

Don haka, bai yiwuwa ka ce “garkuwa ya karye” sai dai “garkuwa ta karye”.

Sai dai akwai kalmomi kadan da wannan doka ta kasa aiki a kansu, wadanda duk da suna da “a” din a karshensu, amma lamarin maza suke da shi, kamar gida, da kuda, da wata da duma.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka'idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri