BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 15:16 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Fassara
 
Fassara

Babban abin da fassara ke bukata shi ne lakanta sosai ta harsunan guda biyu – wanda za ka yi fassara daga gare shi da wanda za ka fassara zuwa gare shi.

Yana kuma da kyau ka san wani abu na al’adun wadanda ke magana da wannan harshe, domin wani lokaci sanin ma’anar kalmomin kawai ba zai ba ka cikakkar fahimtar da kake bukata ba don yin fassara.

A fassara kuma, ma’ana ce ya kamata a fi baiwa muhimmanci ba kalmomin da aka yi magana da su ba.

Misali, Ingilishi da Hausa sun sha bamban da juna. Don haka, ba kome ba ne mutum zai iya fassarawa kai tsaye.

Mu dauki bankwanan bature a lokacin tafiya barci, “Good night”; in aka fassara kai tsaye cewa za ka yi, “Dare mai kyau” abin da zai iya sanya Bahaushe yin dariya idan ya ji.

Amma in ka fassara da “Sai da safe” ko kuma “Mu kwana lafiya”, to a sannan ne Bahaushe zai fahimce ka.

Kuma bature yakan amsa “Good night” ne, ko kuma “Night” kawai, abin da zai kasance shirme a Hausa in ka fassara shi da “Dare” kawai.

Shi ma bature zai ji abu banbarakwai idan ka fassara masa “Ina kwana?” kai tsaye.

Zai yi mamakin inda za ya je ya nemo shi.

Illa dai a yi hattara. Abin da ake fassaruwa kai tsaye, a fassara shi kai tsaye.

Kada neman wata mana ta boye ya sanya a bar ma’ana ta zahiri.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Suna da Mukami
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri