BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 15:20 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Lafazi
 

Yadda lafazin kalmomi ke fitowa daga bakinka shi ne zai sanya mai sauraronka ya fahimce ka ko ya kasa fahimtarka.

Don haka, lalle ka tabbatar kalmomi sun fito daga bakinka dalla-dalla, musamman da yake a rubutun Hausa ba a yin amfani da alamomin karin harshe da za su nuna maka gabàr da za ka ja da wadda za ka gajarta.

Kalmar “bara” in babu wata alama, tana iya nufin “mai yin hidima”, ko “mai rokon abu” ko kuma “shekarar da ta wuce”.

Irin wadannan kalmomi sai a guji amfani da su a farkon jimla, domin ta yiwu kalmar da ka yi zato ba ita ba ce, sai kà dauko karatu sai ka ji bai tafi totar ba.

Ko garuruwan kasar Hausa da ba ka sani ba, kana iya yin kuskuren karin harshe wajen fadinsu.

A nan, ya kamata a tambayi wanda ya sani in akwai.

Haka su ma kalmomin wasu kasashe daban, sai an bincika yadda ake fadinsu kafin fadin sun don maganin kuskure.

Kada ka yi zaton yadda kake karanta babake da Hausa ko Ingilishi haka suke a harsunan wasu kasashen dabam.

Misali in ka ga bakin “j” a kalma, kada ka dauka yadda za ka karanta ta da Hausa haka ake karanta shi a wata kasa.

A kasashen gabacin Turai da dama ana karanta “j” ne a matsayin “y” ta Hausa.

In ka ga Beljejina, za ka karanta ne a matsayin “Belyayina”.

A Spain kuwa ana karanta “j” din kamar “h”. Sunan sarkinsu Juan Carlos, amma za a karanta Juan din ne kamar Huwan.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi
03 Maris, 2009 | News
Suna da Mukami
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri