BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 15:28 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Sabbin kalmomi
 
Sabbin kalmomi

A kullum a fagen watsa labarai muna cin karo da sabbin kalmomi, musamman daga kimiyya da fasaha.

Babban abin da aka fi yi shi ne yi ma masu sauraro dogon bayanin abin da ake magana a kai.

Sai dai ba koyaushe hakan ke wadatarwa ba.

Aiki ne ake bari a baya na samun fassarar da ta dace, wadda kuma za ta karbu, ko wadda ta riga ta karbu.

Wasu kuma kalmomin akan yi zaton babu su ne a Hausa, bayan kuwa akwai su ko makamantansu, bincike ne kawai ba a yi ba sosai.

Don haka, idan bakuwar kalma ta samu, a bincika ko akwai mai ma’anarta a yaren da ake fassara a ciki ko makamanciyarta.

Domin a koyaushe, mutane za su fi ganewa da fahimtar abin da suka riga suka saba da shi.

A yau, kumbon bincike, da ‘yan sama-jannati, da Majalisar Dinkin Duniya da sauransu, suna cikin kalmomin da aka kago, suka dace da al’ada, suka kuma samu karbuwa.

A nan abin hattara shi ne, ba koyaushe ne doguwar fassara ke samun karbuwa ba.

Misali, rediyo mai hoto ko inji mai kwakwalwa, wadanda yanzu galibi jama’a suka yi watsi da su, suka yi aron na Ingilishin suna amfani da su – talabijin da kwamfuta.

Watau dai a yi fassara mai sauki, marar tsawo, wadda mutane za su fahimta, za su kuma iya fadi sauki.

Idan kuma ya zama dole, an yi bincike an ga babu wata kalma da mutane suke amfani da ita, ko wasu masu bincike suka fassara aka kuma ji fassarar ta yi, to lalle fa a yi aro, shi ma yadda zai yi ma jama’a saukin fahimta da saukin fadi.

Harshe tamkar abu ne mai rai da kullum yake kara girma da sabbin kalmomi, da karin magana da fasahohi, musamman ma a wannan zamani na ci gaban kimiyya da kere-kere.

Sai dai idan harshen bai marhabin da ci gaba, yana iya fuskantar hadarin macewa.

Akwai kuma hadarin aro daga harshe daya tilo, abin da ka iya sanya harshen da ake aron daga gare shi, idan mai rai ne, ya zo ya taushe wanda ke aron daga gare shi, idan karami ne.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri