BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 15:36 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Suna da Mukami
 
Suna da Mukami

Bisa al’ada mutane daban-daban suna da kalmomi daban-daban da suke amfani da su don girmama mutum, ko kuma kiran sunan wanda ba a sani ba.

Ana amfani da Malam ko Alhaji, ko kuma Mista. Amma Hausawa, bisa al’ada, suna amfani da Malam din ne ko Alhaji a kan junansu.

Don haka, zai zama bambarakwai a ji ka kira Bahaushe Mista.

Watau dai, ka yi amfani da abin da su mutane suka fi amfani da shi wajen ambaton junansu.

Idan wadanda suka fi kiran kansu Mista ne ka ce masu Mista, masu Malam kuma, Malam.

Misali, Mr Wiston Churchill ko kuma Malam Aminu Kano.

Idan mutum yana da wani mukami, yana da kyau ka yi amfani da mukamin.

Sarkin kaza, shugaba kaza, Dr Wane da sauransu.

Hakan zai taimaka wajen gane mutumin da ake magana a kai.

Sai dai a yi hattara da kalmomin da suka yi kama da fadanci.

Duka dai, wanda ba ka tabbatar da abin da ya kamata ka dosana gaban sunansa ba, gara ka kira shin da cikakken sunansa kawai, don kauce ma abin da mai sauraro zai ji wabai.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri