BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 15:47 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Makarantar Aikin Jarida ta BBC
 
Makarantar Aikin Jarida ta BBC
BBC ta dauki amfani da harshe irin yadda ya dace a aikin watsa labarai da muhimmancin gaske.

Shi ya sanya ta tashi tsaye wajen ganin a koyaushe ma’aikatanta suna la’akari da inganta irin yadda suke amfani da harshe wajen isar da sakon da suke da shi ga jama’a.

Aikin zai inganta. Shi ma kuma amfani da harshen irin yadda ya dace zai inganta.

Shi ya sanya Makarantar Aikin Jarida ta BBC take farin cikin kaddamar da wannan shafi don amfanin masu aikin jarida da ke son inganta yadda suke amfani da harshe a aikin.

Haka su ma sauran jama’a da ke da sha’awa, za su amfana da yadda za su inganta amfani da harshen da kuma sanin wani abu na aikin jarida.

Makarantar ta kuma kaddamar da irin wannan shafi a harsunan Larabci, da Faransanci da sauran harsuna daban-daban da BBC ke watsa shirye-shirye a cikin su.

Aniyar Makarantar Aikin Jaridar ta BBC ita ce ta samar da irin wannan shafi ga dukkan harsuna 33 da take watsa shirye-shirye a cikin su.

Bude wannan shafi matakin farko ne na gurin da muke da shi.

Muna son ganin ya bunkasa sosai, ya zama cikakkar kafa ta kara fahimtar aikin jarida.

Cikin batutuwan da muka taba a shafin a yanzu, har da Rashin Nuna Bambanci, da Rubutu don Rediyo, da Sanin Ya Kamata, da Nahawu, da Ka’idar Rubutun Hausa, da Fassara, da Lafazi, Sabbin kalmomi, da kuma Sunaye da Mukami.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rubutu don Rediyo
03 Maris, 2009 | News
Suna da Mukami
03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri