BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 03 Maris, 2009 - An wallafa a 14:30 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Rubutu don Rediyo
 
Rubutu don Rediyo

Rubutu don rediyo ya sha bamban da rubutu don talabijin, ko jarida, ko ma littafi.

Akwai kuma ka’idojin da ya kamata ka yi la’akari da su.

Babban abu a kowane irin rubutu shi ne mallakar abin cewa, wanda mai sauraro ko karatu zai so sani.

A yi shi dalla-dalla yadda zai yi saukin ganewa. Kada ya zama kwan-gaba-kwan-baya kamar tafiyar kura.

Kada ka yi amfani da kalma biyu ko fi a inda daya za ta wadatar.

Misali, yi amfani da “sananne” maimakon “wanda aka sani sosai”, “watan gobe” maimakon “wata mai kamawa”, “dan kasuwa”, maimakon “mai saye da sayarwa”, “bàra” maimakon “shekarar da ta wuce”, “bana” maimakon shekarar da muke ciki, “badi”, maimakon “shekara mai zuwa” da dai sauransu.

Bata ma mutane lokaci ne ka ce “shekarar badi” bayan ma’anar “badin” ita kadai na nufin shekara mai zuwa. Kazalika babu dalilin cewa “shekarar bana” ko “shekarar bàra”

Duk da haka, wannan ba zai hana ka yi amfani da kalamin da ya fi tsawo ba idan dai shi ne mafi dacewa a wuri.

Lalle ka zam kana da madogara a kan kome, ba shaci-fadi.

Labari cikakke, wanda ka kashe kishirwar mai sauraro, shi ne labari, ba wanda aka bari yana reto ba.

Kada ka bar mai sauraro cewa akwai abin da ya rage ba ka shaida masa ba.

Ka tuna kuma labarin watsawa a rediyo ya sha bamban da na jarida, wanda mutum zai iya komawa baya don sake karanta abin da gane ba ko duba kamus a kan kalmar da bai gane ba.

A rediyo abin da ka fadi ya riga ya wuce ke nan, mai sauraro bai da lokacin yin maimai.

Don haka yi amfani da kalamai masu saukin ganewa, kalmomi gajejjera, masu gaba daya maimakon gabobi biyu, ko biyu maimakon uku.

Su ma jimloli, gajejjera su fi dogaye yawa.

Idan har sai mai sauraro ya tsaya yana tunanin ma’anar wani abu da ka fadi, to ba zai ji sauran abin da za ka ci gaba da fadi ba ke nan.

Ba kuma kamar a talabijin ba, inda mai kallo zai ga hoto, a rediyo kai ne idonsa, da kunnensa, da ma hannunsa da zai taba masa abu ya ji ko kaushi gare shi ko kuma laushi.

A takaice, kai ne za ka siffanta masa kome yadda zai fahimta.

Shi ya sanya amfani da kalmomin yau da kullum, ba masu zurfi ba, ya zama wajibi.

Ba kuma irin wadanda wasu mutane ne kawai suke amfani da su ba – malamai, ko matasa, ko ‘yan wata kungiya, ko soja.

In har ya zama dole ka yi amfani da su, ka tabbatar ka yi bayanin ma’anarsu yadda za a gane.

 
 
WASU SHAFUNAMMU
Rashin Nuna Bambanci
03 Maris, 2009 | News
Sanin Ya Kamata
03 Maris, 2009 | News
Nahawu
03 Maris, 2009 | News
Ka’idar Rubutun Hausa
03 Maris, 2009 | News
Fassara
03 Maris, 2009 | News
Lafazi
03 Maris, 2009 | News
Sabbin kalmomi
03 Maris, 2009 | News
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri