BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 06 Afrilu, 2010 - An wallafa a 13:52 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Hoton bidiyon sanarwar zaben Burtaniya
 
Firayim Ministan Britania Gordon Brown
Firayim Ministan Britania Gordon Brown
Pirayim ministan Birtaniya Gordon Brown, ya yanke shawarar cewa babban zaben kasar zai gudana nan da makonni hudu masu zuwa.

Ya ce, Sarauniya Elizabeth ta biyu, ta amince da rusa majalisar dokoki, kuma za a gudanar da babban zabe a ranar shidda ga watan Mayu.

A karo na farko, jam'iyyarsa ta Labour za ta yi kokarin ganin ta lashe zaben, sau hudu a jere.

Prayim Minista Brown ya ce, yana kira ga 'yan Birtaniya da su zabe shi kai tsaye, domin ya cigaba da aikin farfado da tattalin arzikin kasar.

Sai dai shugabannin adawar kasar - watau David Cameron na jam'iyyar Conservative, ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya, da kuma Nick Clegg na Liberal Democrat - sun yi kiran da a sami sauyin gwamnati.

 
 
Taswirar Najeriya An gabatar da sunayen sabbin ministoci
An gabatar da sunayen sabbin ministoci
 
 
Majalisar zartarwar Najeriya Rushe Majalisar zartarwa a Najeriya
Mukaddashin Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya sallami ministoci.
 
 
Kantin kwari Gobarar kantin kwari
An yi asarar rayuka da dukiyoyin da suka kai biliyoyin Naira
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri