BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 12 Afrilu, 2010 - An wallafa a 18:42 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Jam'iyyar Labour ta kaddamar da yakin neman zabe
 
Fry ministan Birtaniya Gordon Brown
Fry ministan Birtaniya Gordon Brown
A cewar Gordon Brown: "Abinda ke gaba na ne shi ne na farfado da tattalin arzikin Birtaniya"

Irin kalaman da Gordon Brown ya dinga amfani da su kenan alokacin da yake kaddamar da shirin yakin neman zabe na jam'iyyar sa ta Labour, inda yace jam'iyyar na da shirin ciyar da kasar gaba. Mr Brown yace ba shi da aniyar kara haraji a kokarin da yake na farfado da tattalin arzikin kasar.

Alkawuran da ya dauka sun hadar da karin albashi, kara adadin kwanakin hutu ga masu shayarwa da kuma harajin fan 4 a sati na "toddler tax credit" daga shekara ta 2012.

Sai dai acewar Tories sauye-sauyen na labour ba za su yi wani tasiri ba. Ana ta bangaren jam'iyyar Lib Dems cewa tayi, Labour ba da gaske ta ke ba wajen kawo sauyi a fagen haraji da siyasa ba.

Shugaban jam'iyyar Lib Dems Nick Clegg, ya bayyana yadda zai bunkasa kudin shigar da kasar ke samu.

Shi ma jagoran jam'iyyar SNP Alex Salmond, ya kaddamar da nasa yakin neman zaben a Scotland, adai dai lokacin da reshen Labour na Scotland din ya kaddamar da nasa.

Gordon Brown, jagoran jam'iyyar labour

Wani abu da zai ja hankali shi ne na kasancewar wani yaro dan shekara 17 da zai zamo ma'aikacin zabe mafi karancin shekaru a Ingila.

A jawabin da yayi a Edgbaston dake Birmingham, Mr Brown yace jam'iyyar Labour na fuskantar yakin amutu ko ayi rai, yana mai cewa makomar kasar za ta kasance kodai ta masu san cigaba ko kuma ta Conservative.

kalubale

Daga cikin manufofin Labour babu aniyar kara kudaden shiga da haraji kan kayayyakin abinci da kayan sawa na yara.

Editan BBC na fannin siyasa Nick Robinson, yace manufofin sun bayyana bukatar dake akwai na tsauraren matakai, sai dai basu bada cikakken bayanai ba.

Sauran manufofin sun hadar da karin albashi da yin kiranye ga 'yan majalisa da gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a kan sauya tsarin zabe da kada kuri'a a majalisar dokoki kan rage adadin shekarun kada kuri'a zuwa shekara 16.

Tsarin kamfanin Royal Mail

Sakataren kulada harkokin kasuwanci Lord Mandelson, ya musanta zargin cewa Labour ta ya da shrinta na sayar da wani bangare na kamfanin sadarwa an Royal Mail.

Shirin dai ya fuskanci kalubale daga ma'aikatan kamfanin da kuma masu marawa jam'iyyar ta labour baya.

Sai dai acewar jagoran Lib Dems Nick Clegg, " Labour ta yi alkawarin samar da daidaito da sabon tsari na siyasa a shekarar 1997 da 2001 da 2005, kuma yanzu suna kara yi. Idan har basu cimma nasara a shekaru 13 ba, to ta yaya za su cimma a wannan karon".

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri