BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 13 Afrilu, 2010 - An wallafa a 18:56 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Jam'iyyar Conservative ta kaddamar da yakin neman zabe
 
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron, ya kaddamar da manufofin yakin neman zabe na jam'iyyarsa yana mai bayyana su da cewa "shiri ne na kawo sauyi domin ciyar da Birtaniya gaba".

Yace tsari mai kyau shi ne zai samarda ingantacciyar gwamnati wacce za ta baiwa jama'a cikakken iko.

Alkawuran jam'iyyar sun hadar da baiwa jama'a damar kafa makarantu na kansu da hawa kujerar naki waje kara haraji da kuma rage adadin 'yan majalisar dokoki.

Sai dai jam'iyyar Labour ta ce matakan za su bar jama'a ba tare da madafa ba, yayinda Lib Dems suka ce tsarin ya wuce gwana da iri.

David Cameron na jam'iyyar Conservative

Mr Cameron yace manufarsu itace ta sanya jama'a a gaba maimakon manufar da aka sonsu da ita a baya.

Ya kara da cewa zai kare gurabern ayyuka 50,000 tare da karfafa rayuwar bakwai daga cikin ma'aikata goma na kasar idan aka kwatanta da shirin Labour.

Sai dai acewar Labour "shirin Conservative na rage kudaden da gwamnati ke kashewa da fan biliyan 12 ba tsari ne da zai haifarma da kasar makoma ta gari ba.

Manufofin cikin gida

Yace Conservative ka iya gyra rayuwar jama'a ba tare da kashe kudade da yawa ba, abinda yasa take shirin mai da hankali wajen taimakawa talakawa ta hanyar kare shirin lafiya na kasa da samar da ayyukan yi.

"Wadannan manufofi ne da za su samar da sabuwar alkiblar siyasa". A cewar Cameron

Har ila yau manufofin sun hada da baiwa jama'a damar kare kamfanonin aika sakonni musamman wadanda ke fuskantar barazanar rufewa.

Jama'a za su samu damar gudanar da kuri'ar jin ra'ayi kan dukkan al'amura, muddum dai magidanta suka goyi bayan tsarin da kashi biyar cikin dari.

Za kuma abar iyaye da kungiyoyin agaji su kafa makarantu masu zaman kansu a karkashin tsarin da ake amfani da shi a Sweden.

David Cameron da Tony Lit

Wasu daga cikin manufofin jam'iyyar Conservative

Damar mallakar kamfanonin aika sakonni
Rage kudaden da ake kashewa da fan biliyan 6 a 2010/2011
Rage adadin 'yan majalisar dokoki dakashi 10 cikibn dari
Sanye adadin jama'ar da ka iya yin hijira zuwa kasar daga wajen tarayyar turai
Baiwa masu kada kuri'a damar korar 'yan majalisa
Kawar katin shaida
Baiwa iyaye damar

 
 
Janar Babangida Janar Babangida ya ce zai iya tsayawa takara a kowacce jam'iyya
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya.
 
 
Wannan zaben na da mahimmanci sosai Yiwuwar samun ratayayyiyar majalisa a Birtaniya
 
 
Jefa kuri'a Yadda ake zabe
Akalla cibiyoyin kada kuri'u dubu arba'in da biyu za su bude.
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri