BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 13 Afrilu, 2010 - An wallafa a 16:47 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Janar Babangida zai tsaya takara a kowacce jam'iyya
 
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Babangida
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Babangida
Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya tabbatar ma da BBC cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben da za a gudanar a ashekara ta 2011.

Sai dai ya ce duk da cewa shi dan jam'iyyar PDP ne, akwai yiwuwar zai iya tsayawa a wata jam'iyyar.

A karshen makon da ya wuce ne Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasar a zabe na badi. Tsohon shugaban kasar dai, kamar yadda wasu na kusa da shi suka bayyana, ya yanke wannan shawarar ne sakamakon kiraye-kirayen da suka ce wasu `yan Najeriyar na yi masa na ya tsaya takara.

To Hausawa sukan ce 'waka a bakin mai ita ta fi dadi'. Kuma hakane yasa Aichatou Moussa ta tuntubi Janar Babangidan, domin jin ko gaskiya ne zai tsaya takarar?

To muna shaida muku cewa za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Janar Ibrahim Babangidan, a shirinmu na Gane Mani Hanya na ranar Asabar mai zuwa.

 
 
Goodluck Jonathan Ziyarar Goodluck Jonathan zuwa Amurka
Mukaddashin shugaban Najeriya ya kai Amurka
 
 
Jefa kuri'a Yadda ake zabe
Akalla cibiyoyin kada kuri'u dubu arba'in da biyu za su bude.
 
 
Gordon Brown da abokinsa Obama Jam'iyyar labour ta kaddamar da yakin neman zabe
tattalin arziki ne a gaba
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri