BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 30 Afrilu, 2010 - An wallafa a 15:09 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Nazari kan muhawarar karshe ta zaben Burtaniya
 
Shugabannin manyan jam'iyyun Burtaniya
Shugabannin manyan jam'iyyun Burtaniya
An gudanar da muhawara ta karshe kan zabe na kasa baki daya a Birtaniya tsakanin shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar, wato Firaminista Gordon Brown na Jam'iyyar Labour, da David Cameroon na Conservative da kuma Nick Clegg na Liberal Democrats.

Muhawarar ta mayar da hankali ne sosai kan batun tattalin arzikin Birtaniya, inda kuma kowanne daga cikin shugabannin ya bayyana dabarun da zai amfani da su wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Shugaban jam'iyyar Conservative, David Cameron ya ce ba zai taba barin Burtaniya ta shiga sahun kasashe masu amfani da kudin Euro ba kuma ya yi gargadin kar a kuskura a tallafawa kasashen turai da tattalin arzikinsu ke cikin matsi irin su Girka.

Firaminista Gordon Brown kuwa na jam'iyyar Labour cewa ya yi ya nuna kwarewa wurin tafiyar da tattalin arzikin kasar cikin lokacin yalwa da lokacin kunci.

A yayinda Nick Clegg ya sake gabatar da jam'iyyar sa ta Liberal democrats a matsayin jam'iyyar da za ta kwatanta adalci idan an zabe ta .

Malam Sulaiman Baba ma'aikaci ne dake zaune a unguwar Wombwell dake gundumar Barnsley a arewacin Ingila, kuma ya kalli wannan muhawara.

Daga London Muhammad Jameel Yusha'u ya tuntube shi ta wayar tarho dan jin yadda muhawarar ta kasance.

Bayan kammala muhawarar ta uku, kuma ta karshe, kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa, shugaban jam'iyyar Conservative, David Cameron, shi ne yafi nuna kwazo a muhawarar ta jiya.

David Cameron ne a kan gaba

Wannan ne dai karo na farko da aka watsa muhara kai tsaye tsakanin shugabannin jam'iyyun siyasa ta gidajen talbijin a lokacin yakin neman zabe a Birtaniya.

A yanzu dai shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron, shi ne kan gaba, yayinda Nick Clegg na Liberal Democrats ke biye masa baya, sai kuma Firaminista Gordon Brown da yake mataki na uku. A sati mai zuwa ne dai za a gudanar da zaben.

 
 
Jefa kuri'a Yadda ake zabe
Akalla cibiyoyin kada kuri'u dubu arba'in da biyu za su bude.
 
 
Gordon Brown da abokinsa Obama Jam'iyyar labour ta kaddamar da yakin neman zabe
tattalin arziki ne a gaba
 
 
Shugaban jam'iyyar Conservative David Cameron Jam'iyyar Conservative ta kaddamar da yakin neman zabe
kawo sauyi ne a gaba
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri