http://www.bbchausa.com

12 Afrilu, 2010 - An wallafa a 20:43 GMT

Yiwuwar samun ratayayyiyar majalisa a Birtaniya

Idan a misali aka sami ratayayyiyar majalisa bayan zabe mai zuwa, abubuwa da dama ka iya tasowa.

Me ake nufi da ratayayyiyar majalisa?

Ana samun majalisar Hung idan ba a samu jam'iyyar da ke da rinjaye kan sauran jam'iyyu a majalisar ba. Kowacce gwamnati kan fuskanci babban kalubale wajen aiwatar da manufofinta-wadanda suka hada kasafin kudi da dokoki-muddum ba ta da rinjayea majalisa.

A bangaren rinjaye, wanne sakamako za mu so gani?

Ana farawa ne da kogobon kon baya daga Labour zuwa Conservatives na kashi 1.6% cikin dari sannan ya kare a kashi 6.0% cikin dari. Domin samun kashi 6.9% cikin dari, jam'iyyar Conservatives na bukatar samun maki 11 fiye da ta Labour.

Ta yaya jam'iyya maras rinyaje za ta yi mulki a wannan tsari?

Abubuwa da yawa za su dogara ne kan :

. Wacce jam'iyya ce ta samu kuru'u mafiya yawa

. Wacce jam'iyya ce ta samu kujeru mafiya yawa

. To shin jam'iyyar dake kujeru mafiya yawa itace keda kuri'u mafiya yawa( Abune mai yiwuwa Conservatives ta samu kuri'u masu yawa fiye da Labour amma kuma ta samu kujeru kadan saboda banbancin yadda masu kada kuri'a suka maida hankali a baki dayan kasar.)

Wanne karancin rinjaye babban jam'iyya ke bukata?

. Wacce jam'iyya ke da kawance ta fuskar akidu a tsakanin sauran jam'iyyu a majalisar

. Wacce jam'iyya ce keda iko kan digadigen siyasa ( Yana tattare da jam'iyyar data taka rawa a zaben, amma ba zai yiwu ga jam'iyyar data kasa yin katabus a zaben, tayi abu na azo agani bayan an kammala ba.)

. Wacce jam'iyya ce za ta yi karatun ta nutsu wajen bunkasa matsayinta.

Wadannan abubuwa ne dake da alaka da gwamnatin dake da karamin rinjaye, kuma abune mai wahala a cimma daidai to da sauran jam'iyyu domin samun rinjaye.

Idan sakamakon zabe na gaba a majalisar Hung ya baiwa baki dayan jam'iyyu damar taka rawa a gwamnati, sai dai babu kwanciyar hanakali, saboda ya basu damar iko da hukumar ma'aikata da damar gabatar da kuma tasiri kan hukunce-hukuncen majalisa da kasafin kudi dama damar sanya ranar zabe na gaba.

Ya za a yi gwamnatin marasa rinjaye "ta kai labari"?

A wannan yanayi jam'iyyar dake mulki na bukatar hada kai da sauran abokan gamayyar ta domin samun rinjaye a majalisa.

A kwai dai nasarori game da wannan: Zai samar da damar tattaunawa da yanke shawara; har ila yau zai taimaka wajen samar da hadin kai a tsakanin jam'iyyu.

Sai dai akwai matsaloli....jam'iyyar dake mulki za ta fuskanci matsala wajen samun goyon bayan sauran jam'iyyu kan al'amura masu mahimmanci........za ta samu matsala sosai wajen domin shawo kan manufofi masu tsauri.

Wanne misali ne na kurkusa a zaben Westminister?

A bune mai yiwuwa jam'iyya maras rinjaye tayi kokarin jagoranci ta hanyar cimma matsaya da sauran jam'iyyu.

Wannan zai faru ne alokacin da jam'iyya mafi girma ta kulla alaka da kananan jam'iyyu, amma idan alakar bata yi tasiri ba ka iya haifar da matsala.

Alakar da aka kulla tsakanin jam'iyyar Liberal da Labour a shekarun 1977-78, a wannan yanayin gwamnati taki yin aiki da bukatun jam'iyyar Liberal yayinda ita kuma jam'iyyar taki goyon bayan gwamnati kan kowanne al'amura.

Amfanin wannan dai ka iya zamowa ta fuskar daidaito da cimma matsaya da samar da zaman lafiya. Zai kuma karawa kananan jam'iyyu damar fada aji, da kawo tsaiko wajen yanke hukunci.

Zabi ga gwamnatin hadin gwiwa

A tsarin gwamnatin hadin gwiwa, ana raba mukaman ministoci tare da cimma manufa kan al'amuran da za a fuskanta.

Za a kafa gwamnatin hadin gwiwa domin samar da gwamnati mai rinjaye, haka kuma bu ne mai yiwuwa a samar da gwamnatin hadin gwiwa wacce za ta samar da jam'iyya maras rinjaye. Hakan ka iya faruwa ne idan jam'iyyu sama da biyu suka kasa suka mamaye goyon bayan jama'a a kasashen dake da tsarin zabe mai kama da juna.

Gwamnatin Scotland ta shekarun 1999 zuwa 2007 ta gudana ne tsakanin hadin gwiwar jam'iyyun Labour da Liberal Democrats. Haka hadin gwiwar Labour da Plaid Cymru ke jagorantar Wales tun shekara ta 2007. A duka kasashen biyu an asmar gwamnati mai rinjaye.

Nasarori: Tafi ta marasa rinjaye samar da kwanciyar hankali; tare da samar da matsaya wajen yabnke hukunci.

Illoli: rashin kwanciyar hankali; karancin karfin manufofi, rage karfin tattaunawa domin samar da matsaya kan al'amura masu mahimmanci.

Ta yaya za a zabi Pry Minista?

Babu wani tsari takamaimai na zabar Pry Minista bayan babban zabe. Sarauniya ce za ta nemi Pry Minista ya kafa gwamnati, ta hanyar la'akari tanade-tanaden tsarin mulki. Wannan tasri ya bukaci sarauniya ta nemi mutumin da ya samu goyon bayan majalisar wakilai ta kasar.

A zaben da jam'iyya daya ta samu rinjaye a majalisar wakilai, to zabin da ya rage shi ne a nada jagoran jam'iyyar. Idan kuwa babu jam'iyyar data samu rinjaye a majalisa, to tsarin zai kara rikecewa ne kawai tare da daukar lokaci.

A matakin farko Gordon Brown, zai zamo Pry Minista na rukon kwarya duk da cewa ba shi ne jagoran jam'iyya mafi girma ba. Kuma zai kasance babban mai baiwa sarauniya shawara ta fuskar tsarin mulki. Ba za a tilastawa Mr Brown yin murabis ba, har sai ta bayyana cewa mafiya yawan 'yan majalisar sun juya masa baya.

A cewar Lord Butler, Pry Minista mai ci nada damar ya samar da bayanan da sarauniya za ta za ta gabatar.

Abin tambaya anan shi ne wacce jam'iyya ce, ta hanyar hadin gwiwa da sauran jam'iyyu za ta samu rinjaye a majalisar wakilai wajen kada kuri'ar amincewa da kuma samar da sauran kudurori.

Za a samu matsin lamba domin ganin ankafa gwamnati cikin gaggawa- musamman daga jama'a da kuma kafafen yada labarai dama 'yan kasuwa ganin irin bukatun dake akwai na shawo kan matsalar gibi da kuma bashin da kasar ke fama da shi.

Jawabin sarauniya shi ne zakaran gwajin dafi na majalisar da kuma gwamnati. Za a kada kuri'a bayan shafe kwanaki biyar ana muhawara kan jawabin, kuma duk gwamnatin data kasa samun nasara a wannan kuri'a to ta rushe.

To me tarihi ya nuna?

An samu majalisar Hung sau biyar tun daga shekarar 1900.

A lokuta biyu majalisar ta zamio ta Hung saboda an samu sauyin sheka da kuma rashin nasara a zaben cike gurbi. 1996 da 1976.

In banda a lokutan yaki da matsalar tattalin arziki, majalisar Hung a Westminster ta haifar da gwamnatin marasa rinjaye ne maimakon ta jam'iyyu da dama.