http://www.bbchausa.com

13 Afrilu, 2010 - An wallafa a 11:14 GMT

Yadda ake zabe

1. Ranar zabe

Akalla cibiyoyin kada kuri'u dubu arba'in da biyu a fadin Birtaniya za su bude, yawancin su a makarantu da kuma Unguwanni, tun daga karfe bakwai na safe.

Jami'an zabe za su tambayi mai kada kuri'a suna da kuma adireshin sa. Daga bisani kuma sai a soke sunan daga regista, domin kada mutum ya yi zabe sau biyu, domin yin haka ya saba wa doka, kuma za'a iya tuhumar ka da mugun laifi.

A baya dai ana huda kowani katin jefa kuri'a, domin a sa mishi shaidan da zai nuna cewar anyi zabe da shi kuma wani ba zai iya sake amfani da shi ba.

Katin jefa kuri'a dai yana dauke ne sunayen yan takara, da kuma wuraren da suke wakilta, da kuma jamiyyun su. Mai jefa kuri'ar dai zai dauki katin ne, ya nufi wata 'yar rumfa zabe wanda yake so.

Bayan dokar da aka bullo da ita a shekararar 1997, ba a bari jamiyyu sunyi amfani da tambarinsu a kan katin jefa kuri'a, sai dai alamar da su kayi regista da ita a wurin hukumar zabe.

Duk wanda baida jam'iyya zai shaida kansa ne a matsayin Independa, kuma ya bar sashen ba wani rubutu a kai.

An dai sanya wani shirin na musamman, inda kakakin majalisa zai iya sanya sunan 'Speaker' a nasa gurbin, idan kenan yana neman takara kujeran a karo na biyu.

Bugu da kari, dolene kowace cibiyar kada kuri'a ta samu na'urar da zai taimakawa makafi zabe.

2. Kidayar kuri'a

Ana dai kammala zabe ne da karfe goma na dare, kuma za a dauki a akwatin zabe a kai wata cibiya da aka kebe a Unguwar, domin a kirga kuri'un.

Jami'in zaben da aka daurawa alhakin kula da kirgan zai tabbatarda da cewar da an kirga kuri'un da aka jefa a wanan unguwa da gaggawa bayan an gama kammala zaben.

A 'yan shekarun nan, jama'a da dama dai na sun a kidaya kuri'a cikin dare, wasu 'yan kalilan ne suke bari a kada kuri'ar da safe.

A doka dai kamata ya yi hukumar zabe ta kirgi duk kuri'un da ke cikin akwatin zaben, domin a tabbatarda da yawan su ko yayi dai dai da wadanda su ka jefa kuri'a. Idan an kammala wannan matakin ne dai za a raba kuri'un tsakanin 'yan takaran, kamar yadda aka zabe su.

Za a dai gudanarda da wannan kidayan ne a gaban 'yan takaran da kuma wandanda ke wakiltan su. Wannan mataki ne kirga kuri'u a gaban 'yan takara za'a yi shine a kowani rumfun zaben, kafin kuma asake yi a cibiyar tattara kuri'u na wannan yankin.

3. Kuri'un da suka lallace

A wajen kidayan kuri'a ana samu kuri'un da suka lallace, wanda kuma ba a kirgawa da su.

Ana samu kuri'un da suka lallace, inda an same da: basa dauke da allamar katin jefa kuri'a na kwarai; da kuma zaben 'yan takara biyu; ko kuma kuri'ar da ba'a zabi kowa da shi ba.

Jami'in hukumar zabe ne zai fidda wadannan kuri'u da ba a amince da su ba a gaban 'yan takaran, sanan kuma ya bayyana dalilan da ya sa ba za'a amince da shi ba. Babu dai wanda zai iya kalubalantar jami'in hukumar zaben a wurin, sai dai an al'amarin gaban kotun saurarn kararrakin zaben, bayan an kammala zaben.

4. Bayyana sakamako

Bayan an kammala kidayan kuri'u, a gaban wakilin 'yan takara da kuma jamiyyu, ana bukatar jami'in hukumar zaben ya bayyana sakamakon zaben, ba tare da bata lokaci ba.

A baya dai ana samu rige rige na bayana sakamakon zabe a wasu gundomini wasanda suka hada da Torbay da Guilford da kuma Reigate, wadannan gundumoni sune ake bayana sakamakon su na tsawon shekaru talatin da suka wuce.

Samun sakamakon zabe a kan lokaci daga cibiyoyin zabe na taimakawa wajen bayana sakamakon zaben da wuri. Ana dai bukatar an san wanda ya yi nasara a misali karfe biyar na safe na rannar wa shagarin zaben.

Ana ganin, kirga kuri'un zaben bana zai dauki dogon lokaci, saboda sabon ka'idar sa aka bullo da ita na kara tantance masu jefa kuri'a.

5. Sake kidaya kuri'a

Idan am samu cewar 'yan takara sun kusanci juna bisa yadda sakamakon zaben ta kasance, ko kuma dan takara bai samu sama da kashi biyar na cikin dari a kuri'un da aka jefa ba, za a iya nema a sake kidayan kuri'un.

Jami'in hukumar zaben wanda aka daurawa alhakin bayana sakamakon zaben ne yake da hurumin cewar a sake kidayar ko a'a. Su mai da wakilan 'yna takaran dai za su iya nema a sake kidayan kuri'a saboda gudun kada a samu matsala wajen sanya wani dan takara kuri'ar da na nasa ba.

6. Idan 'yan takara sunyi kunnen doki

Idan an sake kidayar kuri'a kuma an samu cewa 'yan takarar sunyi kunnen doki, jami'in hukumar zabe ne dai zaiyi amfani da kwandala, sannan ayi 'yan canke, inda mai rabo sa'a. Duk dan takarar da yi nasara za'a kara kuri'a guda kan wanda aka jefa masa. Sanan kuma a basa kujerar da yake nema.