BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 05 Mayu, 2010 - An wallafa a 16:44 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Yiwuwar samun majalisar da babu rinjaye
 

 
 
Jam'iyyar Conservative ce a kan gaba
Jam'iyyar Conservative ce a kan gaba
Yayinda a yau ake kawo karshen yakin neman zabe a burtaniya, tare da haramar kada kuri'a a gobe Alhamis, wani batu da ke ci gaba da jan hankalin jama'a shi ne na yiwuwar samun majalisar dokoki da babu jam'iyyar da take da rinjaye a cikinta, wato Hung parliament a turance.

Manyan 'yan takarar mukamin Pira Minista uku na kasar dai a yau sun bazama sako sako na kasar don kokarin shawo kan masu zaben da ba su kai ga tsayar da ra'ayinsu a kan wanda za su kada wa kuri'a ba, domin su zabe su.

Da kuma ganin an kaucewa yiwuwar samun majalisar da babu mai rinjaye a cikinta.

Masana harkokin zaben burtaniya dai na cewa, an kwana biyu ba a samu jajiberen ranar zabe mai cike da rudani irin wannan ba.

Binciken ra'ayin jama'a

Idan aka yi la'akari da bincike binciken jin ra'ayin jama'a da dama da aka gudanar don sanin ko wa jama'a za su zaba, wadanda kusan duk suke nuni da cewa babu wata jam'iyya da za ta samu rinjaye a zaben.

Don haka akwai yiwuwar a samu majalisar da babu jam'iyyar da za ta samu rinjaye a cikinta, wato Hung parliament a turance.

Tun makwanni da suka gabata dai ake ta zancen yiwuwar hakan ta faru, sai dai bincike binciken jin ra'ayin jama'a na baya bayan nan sun kara karfafa yiwuwar hakan.

Ko me ya janyo yiwuwar samun majalisar da ba bu mai rinjaye a cikinta, Charlie Haris, wani mai sharhi ne a akan al'amuran siyasar burtaniya

Kuma yace a baya bayan nan, ana samun musanye ne tsakanin Labour da Conservative wajen mulkin kasar, sai dai watakila yanzu mutane su ce fuskoki ne kawai suke sauyawa, ba akidu ba.

Domin babu wani gagrumin banbanci tsakanin jam'iyyun. A don haka mutane za su ce, ba mu son ko wacce daga cikinsu ta samu nasara, muna so ne al'umma ta samu nasara, muna so ne masu zabe su samu nasara.

Hakan ta kara bayyana ne a wata zanga zanga da wasu kungiyoyin kwadago suka gudanar inda suke kiran jam'iyyun su dakatar da kudure kudurensu na zabtare kudaden da ake kashewa wajen samar da ababen morewa rayuwar al'umma, musamman a fannin lafiya.

Dukkan jam'iyyun dai sun nuna cewa za su rage yawon kudaden da suke kashewa a ayyukan gwamnati, sai dai wata ta fi wata ne a yawan abin da za ta rage, abin da ya sa wasu jama'ar ke ganin dukkansu dan juma ne da dan jummai a wannan fannin.

Matukar dai ana son a kaucewa yiwuwar samun majalisa maras rinjaye, to dole daya daga cikin jam'iyyun ta samu nasarar lashe fiye da rabin adadin kujerun da ake da su a majalisar wadanda a yanzu suka karu zuwa dari shida da hamsin daga dari shida da arba'in da shida da ake da su a majalisar da ta gabata.

Rashin samun jam'iyya mai rinjaye a majalisa na nufin, duk jam'iyyar da ta kafa gwamnati, za ta sha wahala matuka wajen zartar da doka a majalisar dokokin, a dai dai wannan lokacin da kasar ke kokarin farfadowa daga rikicin tattalin arziki da take fuskanta.

Makoma

To ko me zai faru idan an samu majalisar da babu jam'iya daya mai rinjaye a cikinta?

Prime Minista mai ci ne dai zai ci gaba da rike mukamin, zai yi kokarin kafa gwamnati ko da kuwa ba jam'iyyarsa ce ta samu kujeru mafi yawa a majalisar ba.

Ga misali, a shekarar 1974, Edward Heath na jam'iyyar Conservative ya ci gaba da rike mulki har tsawon kwanaki hudu, duk da cewa jam'iyyar Labour ce ta samu mafi yawan kujeru a majalisar.

Hakazalika, jam'iyya za ta iya kafa gwamnati duk da ba ta da rinjaye, ta hanayar kawance da wasu jam'iyyun da suke da kujeru da yawa a majalisar, wanda hakan kuma kan samu ne bayan an yi yarjejeniya a kan irin manufofin jam'iyyar kawancen da jam'iyya mai mulki za ta ara ta yafa.

Da alama dai yayinda wasu al'ummar Burtaniyar ke son a samu majalisar da babu jam'iyyar da take da rinjaye a cikinta, saboda in ji su, hakan zai bada damar a saurari ra'ayoyin bangarori da dama wajen zartar da manufofin da za su yi tasiri a kan rayuwar jama'a, maimakon jam'iyya daya dake da rinjaye ta yi gaban kanta.

Sai dai a daya bangaren, jam'iyyar da ta kafa gwamnati a irin wannan yanayi, za ta fuskanci kalubale matuka, wajen ganin ta zartar da manufofin gwamnatinta.

 
 
Gordon Broww Jam'iyyun Burtaniya da akidun su
Akawi yiwuwar ayi kan-kan-kan
 
 
David Cameron na jam'iyyar Conservative Nazari kan shirin zaben Burtaniya
Zaben Burtaniya 2010
 
 
Pira Minista Gordon Brown Tsarin dimokradiyyar Burtaniya
Har yanzu tana kasa tana dabo
 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri