BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 11 Mayu, 2010 - An wallafa a 07:50 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Mutum biyu sun hallaka a jihar Kano
 
A jahar kano dake arewacin Najeria, wata iska mai karfi tare da ruwan sama ta yi sanadiyyar rasuwar mutane akalla biyu da raunata wasu, tare da rushewar sama da gidaje dari.

Wannan lamari dai ya faru ne a daren ranar Lahadi, a Unguwannin Bachirawa da kuma kauyen Kunture dukkansu a karamar hukumar Ungoggo.

Iskar ta kuma yi sanadiyyar karyewar turakun wayoyin wutar lantarki, wato Pole wire.

Sai dai har zuwa yanzu jama'ar yankin sun shedawa BBC cewa babu wani tallafi da suka samu daga hukumomi sakamakon wannan bala'i da ya afka musu

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri