Chelsea na gab da lashe Premier

Chelsea ta dauki gagarumin matakin lashe gasar premier ta Ingila a bana bayan ta lallasa Liverpool daci biyu da nema a filin Anfield.

Chelsea wadda itace bakuwa ta fara wasanne da dari dari kafin a cikin minti na talatin da uku sai Kyaftin din Liverpool Steven Gerrard yayi kuskure abinda kuma ya janyo Didier Drogba ya zira kwallon farko.

Nicolas Anelka a cikin minti na hamsin da hudu ya baiwa Frank Lampard kwallo inda aka samu ci na biyu a yayinda Liverpool ta cigaba da fuskantar rashin nasara a bana.

Wannan nasarar ta nuna cewa dai har yanzu Chelsea ce a saman teburin gasar a yayinda ya rage wasa guda kamalla gasar premier ta Ingila.