Fulham za ta kara da Athletico Madrid

Kungiyar Fulham ta Ingila ta tsalalke zuwa wasan karshe bayan ta samu galaba akan Hamburg ta Jamus daci 2 da 1.

A bugun farko tsakanin kungiyoyin biyu a kasar Jamus an tashi ne babu ci.

A yanzu dai Fulham za ta kara ne da Atletico Madrid wacce ta fitar da Liverpool.

Liverpool ta fita daga gasar ne duk da ta doke Atletico daci 2-1, wanda hakan ke nufin an tashi 2-2 a wasanni biyun da kungiyoyin suka buga.

Wannan dai shi ne karo na farko da Fulham ta kai wasan karshe a gasar Turai.