Warware matsalar masaukin Super Eagles

Dan wasan Super Eagles
Image caption Dan wasan Super Eagles Taiye Taiwo

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta warware matsalar masaukin 'yan wasan Super Eagles a gasar cin kofin duniya da za ayi a kasar Afrika ta Kudu.

A halin yanzu dai Super Eagles zasu sauka ne a otal din Protea Waterfront dake yankin Richards Bay.

Shugaban hukumar NFF Sani Lulu Abdullahi ya shaidawa BBC cewar sun yanke shawarar raba asara tsakanin mahukunta tsohon otal din da aka kama da kuma hukumar ta NFF.

Bayanda aka kammala batun masauki, yanzu dai abinda ya ragewa Super Eagles shine batun wasannin sada zumunci kafin lokacin gasar cin kofin duniyan.