Mourinho ya jijinawa 'yan wasanshi

Kocin Inter Milan Jose Mourinho ya jinjinawa 'yan wasanshi saboda fidda Barcelona a gasar zakarun Turai, inda ya bayyana nasarar a matsayin babbar nasara a tarihinshi.

Mourinho a shekara 1990 ya yi aiki da Barca, amma a wannan karon kungiyar daya jagoranta wato Inter Milan ce ta samu galaba akan Barca daci uku da biyu.

Yace"Na taba lashe gasar zakarun Turai tare da Porto a shekara ta 2004, amma wannan nasarar tafi mani".

Inter Milan zata kara da Bayern Munich a wasan karshe a filin Madrid a ranar 22 ga watan Mayu.

Mourinho ya kara da cewar"shekaru talatin da takwas kenan Inter bata buga wasan karshe ba".