Gary Neville ya sa hanun a kwantaragi

Kyaftin din Manchester United Gary Neville, ya sake sanya sabuwar kwantiragi ta shekara guda.

Dan wasan mai shekaru talatin da biyar, ya shafe kusan watanni 18 baya taka leda sakamakon raunin da ya samu a idan sawu a watan Mayun shekara ta 2007.

Sai dai ya samu takawa Manchester leda har sau 27 a kakar wasanni ta bana, sannan kuma yayi wasanni kusan 600 tun lokacin da ya fara bugawa a shekarar 1992. Wannan yarjejeniyar da dan wasan ya cimma na nufin ya bi sahun Paul Scholes da Ryan Giggs wajen yanke shawarar ci gaba da zama a Manchester United.