'Yan wasan kasar Afrika ta kudu

Kocin Afrika ta Kudu Carlos Alberto Parreira ya sanarda 'yan kwallo ashirin da tara wadanda zasu wakilci kasar a gasar cin kofin duniya da za a fara a Yuni.

Jerin 'yan wasan ya hada da dan wasan West Ham Benni McCarthy da kuma na Portsmouth Aaron Mokoena.

Sai dai Nasief Morris wanda ke taka leda a Racing Santander ta Spaniya baya cikin 'yan wasan da aka kira.

Afrika ta Kudu zata bude fage a gasar da zata dauki bakunci tsakaninta da Mexico a ranar 11 ga watan Yuni a filin Soccer City dake Johannesburg.

Cikkaken jerin 'yan wasan Bafana Bafana:

Masu tsaron gida: Itumeleng Khune (Kaizer Chiefs), Shu-Aib Walters (Maritzburg United), Rowen Fernandez (Arminia Bielefeld, Germany), Moeneeb Joseph (Orlando Pirates).

Masu buga baya: Matthew Booth (Mamelodi Sundowns), Siboniso Gaxa (Mamelodi Sundowns), Innocent Mdledle (Mamelodi Sundowns), Bongani Khumalo (Supersport United), Tsepo Masilela (Maccabi Haifa, Israel), Aaron Mokoena (Portsmouth, England), Bryce Moon (PAOK, Greece), Anele Ngcongca (Racing Genk, Belgium), Siyabonga Sangweni (Golden Arrows Lucas Thwala (Orlando Pirates).

Masu buga tsakiya: Surprise Moriri (Mamelodi Sundowns), Franklin Cale (Mamelodi Sundowns), Lance Davids (Ajax Cape Town), Kagisho Dikgacoi (Fulham, England), Andile Jali (Orlando Pirates), Teko Modise (Orlando Pirates), Reneilwe Letsholonyane (Kaizer Chiefs), Siphiwe Tshabalala (Kaizer Chiefs), Thanduyise Khuboni (Golden Arrows), (Steven Pienaar (Everton, England), Macbeth Sibaya (Rubin Kazan, Russia).

Masu buga gaba: Benni McCarthy (West Ham United, England), Katlego Mphela (Mamelodi Sundowns), Siyabonga Nomvete (Moroka Swallows), Bernard Parker (FC Twente, Holland).