Al Ahly zata kara da Ismailia

Al Ahly
Image caption wasu magoya bayan kungiyar Al Ahli ta Masar

Zakarun kwallon kafa a Masar Al Ahly an sakata rukuni daya da babbar abokiyar hamayyarta Ismailia a gasar cin kofin zakarun Afrika.

Inda aka sakasu a rukunin B tare da JS Kabylie ta kasar Algeriya da kuma kungiyar Heartland ta Najeriya.

A rukunin A kuwa mai rike da kanbum wato kungiyar TP Mazembe ta DR Congo zata fafata ne da kungiyar Dynamos ta Zimbabwe da kuma Esperance ta Tunisia da kungiyar Entente Setif ta Algeriya.

A karshen makon 16-18 ga watan Yuli ne za a fara buga wasanin rukunonin.