Da alamu John Terry ya samu rauni

Terry
Image caption Ingila ba zata ji dadi ba ace Terry ya samu mummunar rauni

Dan wasan baya na Chelsea da Ingila John Terry ya tafi asibiti don a dauki hoton kafarshi ta dama, a yayinda ya rage kasada wata guda a fara gasar cin kofin duniya.

Terry ya samu rauni lokacin horo a yayinda Chelsea ke shirin karawa da Portsmouth a wasan karshe na gasar cin kofin FA.

Sashin yanar gizo na kungiyar Chelsea ya wallafa cewar Terry ya bar filin horonne ba tare da alamun yana fama da matsala ba.

A ranar Alhamis ne ake saran samun sakamakon gwajin da aka gudanar a kafar Terry din.