Kaptin din Chelsea Terry ya koma horo

John Terry
Image caption John Terry na murna tare da sauran 'yan wasan Chelsea lokacin da suka lashe gasar premier

Dan wasan baya na Chelsea da Ingila John Terry ya koma cigaba da horo kuma ana saran zai buga wasan karshe na gasar cin kofin FA tsakanin Chelsea da Portsmouth a ranar Asabar.

An dai samu fargabar cewa dan wasan ya jimu a kafarshi ta dama abinda kuma ake taba tabar shigarshi cikin gasar cin kofin duniya.

Amma dai hoton kafar da aka dauka ya nuna cewar Terry mai shekaru 29 da haihuwa ya koma horo.

Terry yace "Tunda akwai babban wasa dake jiranmu, abinda yafi dacewa shine in saka takalmin kwallo na musamman wanda zai kare mani kafa".

'Yan Ingila dai sun shiga damuwa da farko akan batun Terry ganin irin abinda ya faru da David Beckham da Wayne Rooney a baya.